2 Yuni 2021 - 13:24
Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ( OPEC) Tana Tsumayen Komawar Iran Cikin Kasuwar Danyen Man Fetur

Ministan Man fetur na kasar Iran Bijan Zanganeh wanda ya halarci taron ministocin man fetur da makamashi na kungiyar ta OPEC ta hanyar bidiyo daga nesa, ya bayyana cewa; Taron an yi shi ne a karkashin tasirin shirin komawar Iran cikin kasuwannin duniya.

ABNA24 : A jiya Talata ne dai aka yi taro karo na 17 ta hanyar bidiyo daga nesa na ministocin kasashen kungiyar ta OPEC da wasu kasashen masu arzikin man fetur da ba mambobi ne a cikin kungiyar.

Za a yi taro na gaba ne dai a cikin watan Yuli mai zuwa, kamar yadda ministan man fetur din na Iran ya bayyana.

342/